A wani fefen bidiyo da @jola09217171 ya wallafa shafin Tiktok ya nuna yadda wata ƴar kasar Italiya da ta nuƙi gari tun daga kasar Italiya har zuwa nan Najeriya domin neman mahaifiyarta.
Bayan da ƴar kasar Italiyan suka haɗu da mahaifiyar tata suka fara tattaunawa daga baya da ta gane ita ce mahaifiyarta, ai nan da nan suka shiga cikin shauƙi da mararin junansu ta yin shewa da rungume junansu.
Sanin cewar ƴar tata na da wani tabo a bayanta tun tana jaririya, hakan yasa mahaifiyar tayi gaggawa ta zagaya bayanta sannan ta ɗage rigarta domin ta tabbatar da cewar ita ce ƴar tata.
Bayan mahaifiyar ta ɗage rigar ta kuma yi tozali da wannan tabon a bayannata, nan ta ƙara tabbatar da cewar tabbas ƴar tata ce.
Tayi mamaki matuƙa-gaya, mahaifiyar, domin ta shaidawa majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya cewar rabon da ta saka ƴar tata a idanunta tun a cikin shekarar 1980 lokacin da ta kai ta kasar Italiya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nayi nadamar yin kasuwancin doya – Inji wani mazaunin jihar Legas da aka faɗa masa cewar akwai gwaggwaɓar riba tsababa idan ya siyo doya daga Makurɗi ya siyar a Jihar Legas. Sai dai ya faɗi warwas.
Mahaifiyar ta shaidawa ƴar tata cewar ta sami labarin ƴar tata na hannun gwamnatin kasar Italiyan, hakan yasa tai ta kokari da faɗi tashin samun damar ganinta amma abin yaci tura, domin Jakadancin kasar Italiyan bai bata damar yin hakan ba.
Da farko ƴar taji tsoron taɓa mahaifiyar tata sakamakon yanayin da ta shiga na murna da shaƙuwar na tozali da ƴar tata da ta yi bayan kwashe shekaru aru-aru.
DANNA NAN DOMIN KALLON BIDIYON
Bidiyon ya ja hankulan dayawa daga cikin masu amfani da shafin sadarwa na Tiktok, ga kuma wasu daga cikin ra’ayoyin da majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro muku.
Jeff@F yace: Wannan bidiyon ya kara min ƙarfin gwiwa da yarda da cewar tabbas a kwana a tashi zan haɗu da mahaifina da muka kwashe sama da shekaru 27 bamu haɗu ba.
user3848780488853 yace: Ina fatan nima na haɗu da ƴata.
RichardDiva yace : Ba shakka, akwai kamanceceniya a tsakanin su.
Hildah tace: Duk kanin wata uwa ta san duk kan inda tabo yake a jikin yayanta.
1harlemlilly tace: Ta niko gari dan ta ga mahaifiyarta amma sai ga shi kamar bata ji daɗin ganin mahaifiyar tata ba sai gudunta take.
charlescadogansr yace: Wato ta gane ta ne da tabon dake bayanta tun na haihuwa. Hakan ya burgeni.
cherell Murray yace: ai tun da naga tana ɗaga mata riga na san abinda zai faru.
Akhidenor Liberty yace: Yana da kyau kowa ya kasance yana da wata alama da za a gane shi da ita saboda ba a san abinda gobe zata haifar ba.