By Abbas Yakubu Yaura
Babban bankin Najeriya ya amince da mayar da kudi Naira biliyan 19.3 da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati wanda ta kama daga asusun biyan albashin jihar Kogi dake ajiye a wani asusu.
Kamar yadda wasikar ta bayyana daga babban bankin Najeriya cewa ta samu kudin da wancan bakin ya tura mata za a mayar dasu.
Wata sanarwa a ranar Juma’a ta bakin kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ta nuna cewa mayar da kudaden da CBN zaiyi ya yi daidai da umarnin ranar 15 ga watan Oktoba 2021 wanda mai shari’a Chukwujekwu Aneke na babbar kotun tarayya da ke zamanta a Ikoyi, Legas, inda ya bada umarnin asaki kudin asusun bankin yadda za a iya mikasu zuwa ga CBN.
Hukumar ta shaida wa kotun cewa, mahukuntan bankin, inda asusun yake, sun amince da kasancewar wannan asusu tare da zunzurutun kudi har Naira biliyan 19.3.
Hukumar ta kara jawo hankalin kotun da cewa, har yanzu kudaden da suka kai Naira biliyan 19, 333,333,333.36 na nan a tsare a asusun ajiyar, inda ta kara da cewa, “Hukumomin bankin, sun bi wata wasika mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Satumba. 2021, mai dauke da sa hannun Manajan Daraktanta, ya nuna aniyar mayar da jimillar kudaden da suka kai Naira biliyan 19, 333,333,333.36 zuwa asusun babban bankin Najeriya.
Kazalika Sanarwar mai taken, ‘Boyayyen asusun biyan albashin jihar Kogi na naira biliyan 19.3 ya mayarwa CBN,’ ta bayyana cewa, “matsalar data sake haifar da wata cece-kuce dangane da tushe da kuma mallakar kudaden kuma mafi mahimmanci, ta soke karkatar da kudaden.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A yayin da ake ta cece-kuce kan batun kudaden, gwamnatin jihar Kogi ta musanta mallakar asusun ajiyar inda ta zargi hukumar EFCC da bata masa suna