Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Christopher Musa a ranar Talata ya ce sojoji sun shirya tsaf domin gudanar da zabe a jihohin Kogi, Imo da Bayelsa.
Musa ya yi gargadin cewa ba za a amince da duk wani tashin hankali ba kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa zabukan jihohin uku sun yi tashe-tashen hankula a baya.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta sanya zaben gwamnoni a jihohin uku a ranar Asabar 11 ga Nuwamba, 2023.
Karanta nanYa Kamata A Baiwa Mataimakan Gwamnoni Iko A Hukumance-Ganduje
Da yake jawabi a hedikwatar tsaro da ke Abuja yayin ziyarar farko da Ministan Tsaro Abubakar Badaru ya kai masa, Musa ya jaddada cewa sojoji ba za su yo kasa a gwuiwa ba domin tabbatar da zaben jihohin uku ba tare da tashin hankali ba.
Ya ce mun kuma shirya tunkarar zabe mai zuwa a jihohi uku na Imo, Kogi, da Bayelsa. Ina so in tabbatar da cewa an gudanar da zabukan bisa tafarkin dimokuradiyya, ba tare da tsoro ko fargaba ba.
Ba ma son wani tashin hankali. Ina so in yi kira ga duk masu ruwa da tsaki cewa dole mu tabbatar da cewa an yi zabe cikin walwala kuma an yi zaman lafiya domin sakamakon shi ma ya fitar da abin da mutane ke so.
Musa ya kuma ce gwamnatin tarayya ta ware kudade na musamman domin kula da sojojin da suka samu raunuka a aiyuka daban-daban a fadin tarayya.
A wani labarin kumaAn Bukaci Manyan Yan Siyasar Jahar Zamfara Da Su Daina Bata Sunan Gwamna Dauda
Sai dai Musa ya tabbatar wa shugaban kasar cewa duk da juyin mulkin da sojoji suka yi a yammacin Afirka, sojojin za su kare dimokradiyyar kasar.
Ya ce muna so mu tabbatar wa Shugaban kasa da kai, cewa Rundunar Sojin Nijeriya ta himmatu wajen tabbatar da dimokuradiyya. Za mu yi duk abin da ya kamata don tabbatar da cewa mun kare dimokuradiyyar mu ta asali kuma don ta ci gaba da kuma fadada ta.