Mai baiwa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Shawara na Musamman akan yaɗa labaru Femi Adesina, ya bayyana cewar gwamnati maici a yanzu ta tarar da Najeriya cikin halin rashin tsaro a shekarar 2015.
Adesina wanda yace masu tada ƙayar baya sune matsalar Najeriya a wancan lokacin, amma sauran matsaloli irin su ƴan bindiga daɗi, da garkuwa da mutane, da ƴan ƙungiyar Asiri da sauran su, sune daga baya suka shigo a wannan gwamnatin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sunyi Garkuwa da Daliban Makarantar Cocin Katolika dake Kaduna
Ya bayyana lamarin a matsayin abun baƙin ciki, inda ya ƙara dacewa, Gwamnatin Tarayya na yin aiki tuƙuru domin magance matsalolin tsaro a ƙasar nan.
“Mun tarar da ƙasar nan cikin halin rashin tsaro, akwai kuma zaman lafiya ba daya wa ba, bayan haka, sai matsalar ta ƙaru” Adesina ya shaidawa gidan Talabijin na Channels a ranar Litinin.
“Gwamnati na aiki gadan-gadan, amma wasu naso kada a magance lamarin,” inji Adesina.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar, Ta’addanci, da ƴan bindiga daɗi, da garkuwa da mutane, na yawaita a faɗin ƙasar.
Haka zalika, Mazauna gari da Ɗalibai na Jahohin Arewacin Najeriya sune waɗanda ƴan ta’adda suke kaiwa hari, a yayinda ƴan ta’adda ke kai hari a ofisoshin ƴan sanda a yankin Kudu.