Muna da yaƙini akan Dattakun Kwankwaso – shugabannin NNPP na Kudu maso Yamma
Rikicin da ya dabaibaye Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya dauki wani salo a ranar Juma’a yayin da jiga-jigan Jam’iyyar na shiyyar Kudu maso Yamma suka kada kuri’ar amincewa da goyon baya ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso dan takarar Shugaban ƙasa na Jam’iyyar a 2023.
Jiga-jigan Jam’iyyar sun ɗauki wannan matakin ne yayin wani taron zartarwa na shiyyar Kudu maso Yamma da aka gudanar a Ibadan babban birnin Jihar Oyo.
Dimokuraɗiyya ta tuna cewa tun da farko wani bangare na Jam’iyyar a ƙarƙashin Dokta Boniface Aniebonam ya sanar da dakatar da tsohon Gwamnan Jihar Kano daga Jam’iyyar, amma shugabannin Jam’iyyar na Jihohi shida na shiyyar Kudu maso Yamma sun yanke shawarar ƙin amincewa, tare da jaddada
goyon bayansu da biyayyarsu ga tsohon Gwamnan Jihar Kano.
KARANTA NAN:Iyaye sun koka kan yajin aikin da ake yi a makarantun Gwamnati na FCT
Wasu daga cikin jiga-jigan Jam’iyyar da suka halarci taron sun hada da mataimakin Shugaban Jam’iyyar na yankin Kudu maso Yamma Prince Ademola Ayoade, da Mai binciken kudi na ƙasa Ladipo Johnson, da Shugaban Jam’iyyar na Jihar Osun Dr Tosin Odeyemi.
Sauran sun haɗa da Shugaban Jam’iyyar na Kudu maso Yamma Fasto Peter Olagookun, da Shugaba ta Jihar Legas Mrs Veronica Dikko Kila, da Shugaban rikon Jam’iyyar na Jihar Ekiti Dr Oluyinka Gabriel Folaha, da kuma Shugaban riko na Jihar Ogun Prince Kunle Ibrahim.
Shugabannin Jam’iyyar na yankin yayin da suka ƙi amincewa da Shugabancin Aniebonam, kai tsaye sun yi kira ga duk tsaffin ‘yan jam’iyyar da aka dakatar da su tashi tsaye wajen ƙwato haƙƙin su.
Sun kuma yi kira ga Aniebonam da masu goya mashi baya da su dawo kan hanyarsu domin kaucewa rikici.
Shugabannin jam’iyyar sun kuma yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya musamman waɗanda suka fito daga shiyyar Kudu maso Yamma da su marawa NNPP baya domin samun shugabanci nagari.
A cikin sanarwar da Ayoade ya karanta sun amince da yin duk abin da ya dace don samun kyakkyawan sakamako a nan gaba a Jam’iyyar.
A cewarsu “Mun amince kuma muna goyon bayan ayyuka daban-daban na kwamitin ayyuka na kasa (NWC) da na kwamitin gudanarwa na kasa bayan tantancewa da kuma tantance ayyukan jam’iyyarmu daban-daban a lokacin zaben da ya gabata, kuma mun amince da yin duk abin da ya dace wajen mayar da jam’iyyar ingantacciya.
Haka kuma daukacin kwamitin ya jaddada amincewa da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar NWC na ƙasa (NEC) da kuma shugabancin Jam’iyyar tare da tafiya da Sanata Musa Rabi’u Kwankwaso, tare kuma da yin watsi da kakkausar murya da wasu tsaffin ‘yan jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin Dr Boniface Aniebonam suka yi.
DAILY POST ta rahoto cewa Sakataren Jam’iyyar na Kudu maso Yamma Dr Tunde Oke Jami’in Hulda da Jama’a Kilamuwaye Badmus da Shugaban Jam’iyyar a Jihar Oyo Mista Adeosun Sunday sun yi wata ganawar sirri da Shugaban Jam’iyyar na Kudu maso Yamma Alhaji Adebisi Olopoeyan a gidansa da ke Ibadan.