Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta fara horas da masu ruwa da tsaki kan sabbin tsare-tsare da aka inganta domin inganta sadarwa da saukaka hanyoyin shiga manyan makarantu a yankin Kudu maso Gabas.
Horon mai taken, “Tsarin horas da masu ruwa da tsaki akan manhajar sarrafa kanta, ba da izini da kuma al’amuran gudanarwa na gaba daya” an shirya shine ga shugabannin jami’a Rector’s, Provost, magatakarda, jami’an bada izinin shiga jami’oi da sauran masu ruwa da tsaki.
KARANTA WANNAN LABARIN:Kwankwaso Ya Gana da Wani Ɗan Takarar Shugaban Kasa, Sun Fara Batun Kulla Kawance a 2023
Da yake sanar da bude horaswar a Enugu, magatakardar hukumar ta JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana cewa horon zai baiwa mahalartan damar yin amfani da tsare-tsaren da aka tsara domin dinke barakar sadarwa tsakanin hukumar, NUC, NABTEB, hukumomin manyan makarantu.
Oloyede, wanda ya halarci taron ta dandalin Zoom, ya bayyana cewa horon zai fadakar da cibiyoyi da hukumomin da ke kula da yadda ake amfani da tsarin hada-hadar kudi da tsarin koyarwa IBASS da CAPS.
Ya ce hukumar ta himmatu wajen saukaka hanyoyin karbar karatu a manyan makarantu da kuma dakile tafka kura-kurai a sassan ilimi a fadin kasar nan.
Don haka ya umarci cibiyoyi da su yi amfani da hanyoyin da za su iya amfani da su, ya kuma kara da cewa dandalin ya samar da hanyar sadarwa mai kyau tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin.
“Makasudin horon shine domin a ba ku sabbin tsare-tsare na hukumar. An yi yunƙurin don sauƙaƙe hanyoyin shigar da su da kuma haifar da yanayi mai daɗi. Mun samar da CAPS ne domin ba wa manyan makarantu da hukumomin gudanarwa da JAMB damar yin mu’amala mai kyau da kuma tabbatar da cewa babu gibi a tsarin shigar da dalibai da kuma tantance kwasa-kwasai,” inji shi.
Ita ma da take magana daraktan hukumar ta JAMB ta shiyyar Kudu maso Gabas, Misis Ebere Okeke, ta ce an horas da su ne domin tabbatar da tsarin shigar da makarantun gaba da sakandare cikin sauri, gajarta da kuma tsarin shiga jami’o’i a Najeriya.
“Hukumar tana aiki tare da NABTEB, NCC, da sauran hukumomi da cibiyoyi. Yanzu muna cikin dandali daya kuma duk bayanan da masu shiga za su samu shine abin da VC da hukumomin da ke kula da JAMB za su samu.
“ CAPS, an tsara shi ne don jagora da inganta sadarwa da musayar bayanai tsakanin hukumar da masu rijistar hukumomi da kuma dinke barakar sadarwa da ake samu a baya tsakanin hukumomin.
Tun da farko a jawabin maraba, mataimakin shugaban jami’ar Nsukka ta Najeriya, Farfesa Charles Igwe ya yabawa Jamb bisa wannan shiri, inda ya kara da cewa hukumar a kodayaushe tana kan gaba wajen tantance matakai a fannin ilimi.
Ya bada tabbacin kungiyar masu ruwa da tsaki wajen samun nasarar shirin.
Mahalarta taron wadanda akasari sun hada da mataimakan shugabannin jami’oi, Rectors, Provost, Magatakarda da jami’an bada izinin shiga jami’a , an zana su a fadin jihohi biyar na shiyyar, da suka hada da jihohin Anambra, Abia, Enugu, Ebonyi da kuma Imo.
A wani labarin kuma, Majalisar Dattijai Ta Yi Barazanar Kame Babban Sakataren Ma’aikatar Kudi Kan Batan N113m Na Hukumar JAMB
Majalisar dattijai ta yi barazanar sammacin kama babban sakataren ma’aikatar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa idan Daraktan Ma’aikatar Kudi ya kasa gabatar da wasu muhimman takardu da suka shafi fitar da Kuri’u masu fa’ida da kuma batan Naira miliyan 113 na albashin hadin gwiwa na Hukumar JAMB.
Da yake magana a ranar Talata a Abuja, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Gwamnati, Sanata Matthew Urhoghide (PDP, Edo ta Kudu), ya bayyana cewa barazanar ta zama wajibi saboda rashin halartar Daraktan da ya yi watsi da gayyata har sau uku.