Musulmai sun yi dandazo a babban masallacin kasa na Abuja a ranar Juma’a tare da gabatar da addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya da ci gaba a daidai lokacin da Najeriya ke bukin cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai a ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba.
Imam Dr Muhammad Kabir, wanda ya jagoranci sallar ta musamman, bayan da ya gudanar da sallar Raka’a ta jam’i guda biyu, ya ce hudubar ta yau tana kira ga ‘yan Najeriya da su dage wajen hadin kai da zaman lafiya.
Karanta nanShaye Shayen Miyagun Kwayoyi Ke Haddasa Hadurra A Najeriya-FRSC
Ya kamata su ci gaba da kasancewa cikin hadin kai da aiki tukuru domin rayuwa ta gyaru da kyau mu mutunta gwamnatin wannan lokaci domin samun nasarar wannan gwamnati.
Dole ne ‘yan Najeriya su nuna godiyar su ga Allah da ya ci gaba da zama kasa daya mai cin gashin kanta.
A cikin wa’azin, Kabir ya kuma yi kira ga kungiyar kwadagon da ke shirin shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a mako mai zuwa, da su duba tare da sake duba batun yajin aikin da suke yi, maimakon haka su sa gwamnati ta ci gaba da tattaunawa.
Tabbas yajin aikin zai jefa rayuwar talakawan kasar nan cikin hadari kuma wannan shi ne rokonmu gare su,” in ji Imam.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa masallacin kasa ne ya shirya taron addu’o’i na musamman a wani bangare na gudanar da bukukuwan zagayowar ranar samun ‘yancin kai.
Kabir ya yi addu’ar Allah ya yi wa shugabannin kasar nan jagora wajen yanke shawarwarin da za su shafi rayuwar ‘yan Nijeriya da dama, ya kuma taimaka wa kasar ta shawo kan wasu matsalolin da ake fuskanta, musamman ta fuskar rashin tsaro, cin hanci da rashawa da kuma tattalin arziki.
A wani labarin kumaHukumar Kwastam Ta Samarwa Gwamnatin Tarayya Naira Biliyan 343 A Cikin Wata Daya
Taron addu’o’in ya samu halartar Shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunci da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Namadi Sambo. .
Sauran sun hada da Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, Wakilan Hafsoshin Sojoji da Sufeto Janar na ‘yan sanda da kuma jami’an Diflomasiyya. (NAN)