Najeriya ta zo ta daya a jerin kasashen da aka fi shan Wiwi a duniya, Buba Marwa Shugaban Hukumar Yaki da Fasakwabrin Miyagun Kwayoyi, Mohammed Buba Marwa ya ce Najeriya ce tazo ta daya a jerin kasashen da su ka fi shan wiwi a duniya, LIB ta ruwaito.
KU KARANTA: Hukumar NDLEA ta kama buhun tabar wiwi 35 a Rivers, ta kama mutun daya
A cewarsa akwai ‘yan Najeriya miliyan 10.6 da su ke sha. Ya bayyana hakan ne yayin jawabi a Taron tattaunawa kan lafiyar kwakwalwa na Vanguard kashi na biyu.
Yace akwai ‘yan Najeriya da yawa da ke shan wiwi kuma ba a san hakan ba sai shekarar 2018 da UNODC tayi bincike akai.
Kafin nan ba a san yadda lamarin yake ba a Najeriya. Kuma a cewarsa hakan ne ya kara bude idon hukuma kan yadda ake shan wiwi a kasar.
Beraye Sun Cinye Tabar Wiwi Kilogram 200 Da ‘Yan Sanda Suka Kama Daga Hannun Dilolin Muggan Kwayoyi
Kotu ta saurari yadda berayen a wasu lokuta suka cinye tabar wiwi da aka ajiye a matsayin shaida.
Alkalin ya kawo wasu kararraki guda uku da beraye suka lalata tabar wiwi da aka ajiye a matsayin shaida.
Wata sanarwa da aka karanta wa kotun ta ce: “Beraye kananan dabbobi ne kuma ba sa tsoron ‘yan sanda. Yana da wahala a kare muggan kwayoyin daga gare su. “