Cibiyar dake kula da manyan cututtuka ta ƙasa ta bayyana cewa, an samu sabbin mutane 255 da suka sake kamuwa da cutar Covid-19, da mutuwar mutane 4 a ƙasar cikin awanni 24.
A cewar cibiyar ta NCDC, wannan ya sanya an samu adadin mutane dubu ɗari 204, 456 da suka kamu da cutar a Nigeria, kamar yadda majiyar jaridar Dimokuraɗiyyar ta ruwaito.
Daga cikin inda aka samu sabbin waɗanda suka kamu da cutar akwai, jahar Imo da mutane 124, sai jahar Lagos da mutane 72, da Babban birnin tarayya Abuja da mutane 36, sai jahar Rivers da mutane 16, sai Enugu da mutane 6, da kuma mutum ɗaya a Kano.
Kimanin mutane dubu ɗari 192,620 aka yiwa magani sakamakon kamuwa da cutar, a yayinda waɗanda suka rasu sakamakon cutar ya kai dubu 2,677.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hadarin Mota da Mashin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2 a Ondo
A halin yanzu Nigeria ta tabbatar da kamuwar mutane dubu ɗari 204,456 ga cutar, da Jahohi Lagos da Babban birnin tarayya, da Rivers, da Filato da mafi yawan waɗanda suka kamu da cutar, tun bayan lokacin da aka samu ɓarkewar Covid-19 a ƙasar.