By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane bakwai ne suka jikkata a ranar Juma’a a wata arangama tsakanin ‘yan sanda da magoya bayan tsohuwar jam’iyya mai mulki a Guinea-Bissau.
A cewar manema labarai, lamarin ya afku ne a Bissau babban birnin kasar da ke hedikwatar jam’iyyar Afrika mai ‘yancin cin gashin kai ta Guinea da kuma Cape Verde daura da fadar shugaban kasa.
DUBA WANNAN LABARIN: Na Shararawa Matar Obiano Mari Don Kare Kai Na, Inji Bianca Ojukwu
‘Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da harsashi wajen tarwatsa magoya bayan jam’iyyar PAIGC, wacce ta jagoranci kasar Guinea Bissau tun daga samun ‘yancin kai daga kasar Portugal a shekarar 1974, wanda kuma har yanzu ta tsaya takara a zaben shekarar 2019 na shugaba Umaro Sissoco Embalo.
“Mun yi tir da abubuwan da suka faru a wannan maraice. Jami’an tsaron sun kutsa cikin hedkwatar hukumar ta PAIGC inda ake gudanar da taron kwamitin tsakiya na jam’iyyar,” kamar yadda kakakin jam’iyyar, Joao Bernardo Vieira, ya shaida wa manema labarai.
‘Yan jam’iyyar sun taru ne domin shirya taron jam’iyyar daga ranar Asabar zuwa Talata amma wani abokin hamayyar shugaban jam’iyyar, Domingos Simoes Pereira, ya dauki matakin shari’a don hana gudanar da taron.
Wata kotu a yankin ta haramta taron jam’iyyar sannan dan takarar jam’iyyar Bolom Conte, ya yi kira ga ‘yan sanda da su aiwatar da hukuncin kotun.
Vieira ya ce “Hukumomin shari’a suna buƙatar PAIGC da ta mutunta hukuncin kotun yankin Bissau,” in ji Vieira.
A watan da ya gabata ne wasu ‘yan bindiga da suka rufe fuska suka kai hari a hedikwatar hukumar ta PAIGC, makonni bayan wani yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a kasar da ke da mutane miliyan biyu.
A ranar 1 ga watan Fabrairu, wasu mutane dauke da muggan makamai sun kai hari kan gine-ginen gwamnati a Bissau a lokacin da shugaban ke jagorantar taron majalisar ministocin kasar. An kashe mutane 11 a harin.
AFP