By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Alhamis din data gabanta ne aka tabbatar da mutuwar wata mata a wani hatsarin mota da ya afku a unguwar Babale da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.
An tattaro cewa wasu biyu sun samu raunuka kuma an garzaya da su asibitin kwararru na jihar Filato da ke birnin Jos.
Wasu Shaidun gani da ido sun bayyana cewa hatsarin wanda ya rutsa da wata motar tanka da kuma babur mai Keke Napep ya afku ne da misalin karfe 4 na yamma.
Wani mazaunin garin Babale, Musa Ibrahim, wanda ya halarci aikin ceto wadanda suka tsira da ransu ya ce, “An yi wani hadari a yau (Alhamis) a unguwarmu da ke Babale da misalin karfe 4 na yamma. Motar tanka da keke Napep hatsarin ya rutsa dasu.
“Wata mace, mazauniyar Zakaliyo ta rasa ranta. Wata matar da ke tare da direban Keke Napep ta samu raunuka sakamakon karaya.
“An kai su asibitin kwararru na jihar Filato domin ci gaba da basu kulawar likitoci.
“Mun dauki sama da sa’o’i uku kafin mu kubutar da direban motar dakon mai wanda ya makale a cikin motar sai da muka nemi taimakon wata karamar mota da kuma wani tip don taimaka wajen dagawa da janye kan motar kafin a ceto shi da ransa. An kuma garzaya da shi zuwa asibiti”.
Sai dai kokarin jin ta bakin kwamandan hukumar ta FRSC na jihar Filato Alphonsus Godwin yaci tura amma wani jami’in hukumar da ba ya son a ambaci sunansa ya tabbatar da faruwar hatsarin ga manema labarai a Jos ranar Alhamis.
Jami’in da ya danganta hatsarin da wuce gona da iri ya ce, “Eh, hadarin ya faru kuma abin takaici, mutum daya ya rasa ranta.”
Ya kuma bukaci direbobin tanka da sauran masu amfani da hanyar da su kula da ababen hawansu yadda ya kamata tare da gujewa gudun wuce gona da iri domin dakile hadurran da ke tattare da rashin bin ka’idar tuki.
Ya kara da cewa “Muna son duk masu amfani da hanyar su yi amfani da wayarws da kan da ake yi musu domin amfanin kansu da kuma kare lafiyarsu.”