Wasu mutane 10 da aka yi garkuwa da su a wata gona da ke Ayede- Ogbese, a karamar hukumar Akure ta Arewa a jihar Ondo, sun samu ‘yanci daga karshe.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ondo, DSP Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da hakan a wata tattaunawa da ta yi da gidan Talabijin na Channels ta wayar tarho a Akure. Ya ce wadanda lamarin ya rutsa da su sun sake samun ‘yancinsu da sanyin safiyar Laraba.
An tattaro cewa wasu mutane dauke da makamai sun yi garkuwa da wani manomi mai suna Femi Alawiye da wasu ma’aikatansa a gonarsa da yammacin ranar Asabar.
An ce masu garkuwar sun yaudari wadanda abin ya shafa zuwa gona da cewa gonar tana ci da wuta.
Wani dangin manomin ya bayyana cewa sa’o’i kadan bayan sace su, masu garkuwan sun tuntubi iyalan, inda suka bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 100 wanda daga baya suka rage zuwa naira miliyan 10 bayan tattaunawa da yawa.
Ko da yake, ba a iya tabbatar da ko iyalan wadanda aka sace din sun biya kudin fansa domin a sako su ba.
Comments 1