Gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa daga farkon wannan shekara {2022} zuwa wannan lokaci, ta kashe naira Miliyan 800, wajen samar da magungunan yaki da cutar zazzabin cizon sauro a jihar.
Kwamishinan lafiya na Kano, Dr Aminu Tsanyawa ne ya bayyana hakan a yau Talata, yayin kaddamar da zagaye na biyu na bayar da riga kafin cizon sauron ta hanyar bayar da gidan sauro mai magani.
Kazalika tallafin ya kuma kunshi kayan da za’a baiwa mata masu juna biyu, da kuma jariran da zasu Haifa, dama sauran kananan yara, wanda kuma taron ya gudana a jihar Kano.
Ya kara da cewa maganin sauron za a rabar das hi ga cibiyoyin kula da lafiya dake jihar guda 1,586, wanda kuma ya kunshi mutanan gari musamman mata da kananan yara.
‘`Daga watanni hudun farkon shekarar 2022, mun samu rahotanni da suka danganci cutar zazzabin cizon sauro 336,896, kuma tuni cikin mutanan da dama suka samu lafiya, yayin da 96 suka rasu.’’ Inji Tsanyawa.
Kwamishinan ya kara da cewa cutar zazzabin cizon sauron yanzu ya zama wani abun takaici, duba da yadda kullum take kara ta’azzara, lamarin dake bukatar kara hada karfi wajen yaki da cutar.