A ranar Litinin din da ta gabata ne rundunar sojin kasar ta sanar da cewa mutane 5 ciki har da dan sanda guda ne aka kashe a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo lokacin da aka umarci sojoji da su yi luguden wuta kan jama’a.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce babban hafsan sojin da ya ba da wannan umarni yana cikin ayarin motocin da suka nufi garin Bunia — babban birnin lardin arewa maso gabashin Ituri — lokacin da lamarin ya faru a ranar Lahadi.
Sanarwar ta kara da cewa, an samu tashin hankali kafin harbe-harbe sakamakon rashin fahimtar juna tsakanin sojojin da ke tare da jami’in da ba a bayyana sunansa ba da kuma wasu jami’an tsaro da ke tare da shingen bincike a kan hanya.
“Wani jami’in soja mai mukamin kanar ya umurci sojoji da su yi harbi a cikin jama’a bayan da aka samu rashin fahimtar juna a garin Luna da ke tsakanin lardin Kivu ta Arewa da Ituri. An kashe mutane uku ciki har da dan sanda guda a nan take, yayin da wasu biyu suka mutu. a asibiti,” Kyaftin Anthony Mualushayi, kakakin rundunar soji a arewacin Kivu, ya shaida wa manema labarai.
An kai wasu mutane da dama da suka jikkata zuwa asibitoci a garuruwan Eringeti da Oicha da ke kusa.
Mualushayi ya kara da cewa an kama jami’in sojan ne domin gurfanar da shi gaban kuliya