Dr Rilwanu Mohammed, Chairman, shugaban hukumar lura da lafiya a matakin farko na jihar Bauchi, BASPHDA, ya ce mutum 22 cikin 57 ne suka mutu sakamakon cutar Lassa a jihar Bauchi a cikin shekarar 2020.
Rilwanu ya tabbatar da hakan ne a ranar Litinin a yayin zantawa da manema labarai a Bauchi. Ya kara da cewa cibiyar lura da lafiyar ta yi ayyukan dakile cutar a gidaje 6, 000 da kuma kasuwanni, da kuma rijiyoyi, domin dakile cutar.
Ya ce wannan matakin da suka dauka ya rage yaduwar cutar ta Lassa, inda a 2021 mutum uku kawai suka kamu da cutar.