Fitaccen Mawaƙin Nan Ɗan Asalin Ƙasar Ghana Charles Mensah Wanda akafi sani da Shatta Wale ya bayyana cewar ya gwammace ya jefar da kuɗin sa akan titi, daya kaisu Coci domin hadaya.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar a tattaunawar da akayi dashi a gidan rediyo, Mawaƙin ya bayyana cewa Allah ya taimake shi sosai a harkar shi ta waƙa, wannan ne ya sanya yake godiya ga masoyan sa na Asali.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ma’aikatan Majalisar Dokokin Kasa Sun Nuna Rashin Amincewarsu Da Rashin Biyan Mafi Karancin Albashi
Yace ” mutane na faɗin abubuwa da yawa a kaina, amma mi ka sani a kaina, wasu baza su gani ba, akwai wanda ke son taimakon Shatta, kuma in naje wani wuri suna taimako na.
Mawaƙin yace ya yi imani sosai akan titi, ya ƙara dacewa “na gayawa kai na cewa duk ranar da zan kai wata kyauta a coci, to na gwammace in kaita akan titi.
Shatta shine wanda ya lashe gasar mawaƙin da yayi fice a ƙasar Ghana a shekarar 2014 a taron Vodafone na mawaƙa.
Ƴan ƙasar Ghana na ganin girmansa sosai a masana’antar waƙa.
Comments 1