Wani mai laifi Ibrahim Abdullahi da aka yankewa hukuncin daurin shekara daya a gidan yari bisa samunsa da laifin satar kudi N30,000, ya amsa laifin yin musanyar katin ATM don samun kudin daurin aurensa.
Abdullahi ya fuskanci tuhume-tuhume biyu na sata da hukumar yaki cin hanci da rashawa ta EFCC shiyyar Gombe ta gabatar a gaban kotu.
Karanta nanMahaifiyar Tsohon Kakakin Majalisa Yakubu Dogara Ta Mutu
A wata sanarwa da EFCC ta fitar a ranar Juma’a, ta ce mai shari’a M.A Shambu na babbar kotun jihar Bauchi da ke zamanta a Bauchi a ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba, 2023.
Ya yanke wa Ibrahim Abdullahi hukuncin daurin shekara daya a gidan yari bisa samunsa da laifin satar kudi N30. 000 ta hanyar zamba ta hanyar musanya katin ATM na cirar kudi a banki.
An karantowa wanda ake zargi laifinsa kamar haka kai Ibrahim Abdullahi ka yi satar kudi a wani matin ATM mallakin Zainab Usman, ta hanyar amfani da katin ATM din ta na UBA wanda ya sabawa sashe na 287 na dokar Penal Code.
Ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, wanda ya sa lauyan EFCC A.B. Kware ya bukaci kotun da ta yanke masa hukunci tare da yanke masa hukuncin da ya dace, yayin da lauyansa Jamilu Salihu ya roki kotun da ta yi adalci da jin kai.
Ya bayyana cewa wanda yake karewa ya kasance mai laifin farko wanda ya yi alkawarin daina aikata wannan laifi da ake tuhumarsa dashi.
Mai shari’a Shambu ya yanke wa Abdullahi hukuncin daurin shekara daya a gidan yari ko kuma ya biya tarar Naira 20,000 da kuma mayar da Naira 30,000 ga wadda keda katin ATM din.
A wani labarin kumaKirsimeti: FRSC ta Gargadi Direbobi Kan Amfani da Tayoyin da Wa’adinsu Ya Kare
Ya yi mata tayin taimaka mata wajen sarrafa ATM bayan ya mika masa katinta, sai ya saka a cikin injin, ya ce kudin basu fita ba sannan ya mayar da katin sai dai jim kadan bayan ta dawo gida ne ta samu shedar zare kudi naira 30,000 sannan ta gane cewa katin Abdullahi ya dawo ba nata bane.
Yayin da ake kama shi da kuma yi masa tambayoyi, Abdullahi ya bayyana cewa ya taso ne daga jihar Kano zuwa jihar Bauchi domin yin musanya da katin ATM don samun kudin daurin aurensa.
Ya kuma bayyana cewa shi ne ya aiwatar da wannan aika-aika da kan sa sannan kuma katunan ATM daban-daban guda biyar da aka samu a hannun sa na wadanda abin ya shafa ne.