Na yarda da nasarar ka — Amaechi ya taya Tinubu Murnar Lashe Zaɓen APC
Tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya taya Jigon Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu akan nasarar daya samu na zama Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar.
Amaechi a cikin wata takarda, ya bada tabbacin goyon bayan sa a lokacin Zaɓen Shugaban Ƙasa a Shekarar 2023.
Tinubu ya kada Abokanan hamayyar sa guda 12, sa suka haɗa da Amaechi, da Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, inda ya samu Tikitin APC.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Buhari zai yiwa Ƴan Najeriya jawabi a ranar Lahadi
Tinubu, da yayi takarar Samun Tikitin Takarar Shugaban Ƙasa da ƴan Takara 13, ya samu ƙuri’u 1,271 a zaɓen, inda ya yi nasarar lashe zaben Fidda Gwani na Shugaban Ƙasa.
Amaechi, tsohon Gwamnan Jahar Rivers, ya zo na biyu da ƙuri’u 316, a yayinda Osinbajo yazo na uku da ƙuri’u 235
Comments 1