Rundunar sojin saman Najeriya ta sake kai harin bam a wani sansani na wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Dan-Karami, a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Majiyoyi sun shaidawa jaridar PUNCH cewa ‘yan bindigar da dama sun rasa rayukansu a lokacin da aka kai harin bam a sansanin a ranar Alhamis.
Wani mazaunin garin Musa Shehu ya ce daga nesa ya hango hayaki yana fitowa daga sansanin.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Bukaci ASUU Da Tabi Umarnin Kotu Nan Take Ta Janye Yajin Aiki
“Rundunar sojin saman Najeriya ta kai wa sansanin hari a yammacin jiya (Alhamis) kuma muna iya ganin hayaki daga wannan wajen.”
Shehu ya ce sun kuma ji karar tashin bama-bamai a yayin da jirgin yakin sojin sama ke jefa bama-baman a sansanin Dan-Karami.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a iya tantance ko Dan-Karami na cikin ‘yan fashin da aka kashe ko a’a ba.
Dan-Karami shugaban ‘yan bindiga ne da ke addabar al’ummar jihohin Zamfara da Katsina.
A wani labarin kuma, An kama Tsoho mai shekaru 68 da ya yi lalata da ƙaramar yarinya a Osun
An gurfanar da wani mutum mai shekaru 68, Ayodele Faremi, a gidan yari bisa zarginsa da lalata da wata yarinya ‘yar shekara 10 a Osogbo, babban birnin jihar Osun.
An kama Faremi ne a ranar Lahadi bayan da aka kai karar ofishin ‘yan sanda na Dada Estate, Osogbo.