- Hukumar NAFDAC ta cafke wani mai sana’ar sayar da kayan ganye na maganin gargajiya a Ibadan dake jihar Oyo
- Sashen sa ido na hukumar ne ya dauki matakin damke wanda ake zargin domin a kawo karshen sana’ar haramtattun magungunan gargajiya masu cutarwa.
- Rashin ingancin samfurin kayan ganyen gami da rajista da hukumar tasa akayi ram dashi.
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa ta kama wani mai sana’ar sayar da kayan ganye na maganin gargajiya a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, Abdulroheem Ajao,Punch ta rawaito.
Sunan haramtaccen maganin kayan ganye shine At-Taqwah Herbal Medicine.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tonon Silili: Shugaban EFCC, Ya Roke Ni In Bashi Dala Miliyan Biyu — Matawalle
Hukumar ta kuma rufe kantin sayar da maganin gargajiyar na kayan ganye na Ajao mai daki takwas da ke bayan Kwalejin Model Periscope, Unguwar Musulmi ta Ibadan.
Daraktar NAFDAC Kudu-maso-Yamma, Misis Florence Ajayi ce ta jagoranci tawagarta zuwa inda ake sarrafa kayayyakin maganin gargajiyar na kayan ganyen ba bisa ka’ida ba.
Ta bayyana cewa doguwar hannun doka ta kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton sirri na mutanen da ke zaune a yankin.
Ajayi ta ce, bayan da al’ummar yankin suka sanar da hukumar ta NAFDAC wannan haramtacciyar hanya, sai sashen sa ido na hukumar ta dauki matakin damke wanda ake zargin domin a kawo karshen sana’ar haramtattun miyagun kwayoyi masu cutarwa.
“Al’umma a nan sun bawa hukumar mu shawara. Sakamakon ziyarar ya nuna cewa yanayin da ake samarwa da magungunan gargajiya na kayan ganyen ba shi da tsafta,” in ji Ajayi.
Ajayi ta ce rashin kulawa da jahilci ne ya haifar da gurbatattun magunguna a kasar nan.
Ajayi ta kara da cewa samfurin ba shi da rajista da hukumar.
“Akwai matakai guda uku don yin rajista da suka hada da takardu tare da biyan kuɗi, nazarin dakin gwaje-gwaje da rahoto don amincewa, amma kamar yadda na ke magana babu wata rajistar da akayi kwata-kwata tare da NAFDAC.”
Yayin da yake amsa aikata laifin, Ajao ya ce ya yi matukar mamakin yadda aka kama shi bisa zargin samar da magungunan kayan ganye marasa inganci.
Wanda ake zargin ya bayyana cewa ya shafe sama da shekaru biyar yana gudanar da aiki a yankin, inda ya rabar da shi cikin nasara a fadin yankin Kudu maso Yamma na kasar nan.
Ya kara da cewa kayayyakin da yake amfani da su na maganin sun hada da hawan jini, zazzabi, tabarbarewar jima’i, da sauran cututtuka masu alaka.
Ajao ya yi ikirarin cewa ya nemi amincewar hukumar ta NAFDAC kan kudi naira 500,000, tare da takardar shedar daga hukumar kula da harkokin kamfanoni a Najeriya.
Ya ce, “Muna samar da kayan maganin gargajiya, Muna raba wa jihohin Jos, Legas da sauran sassan kasar nan. Na shafe kimanin shekaru biyar ina wannan sana’ar. Sunan maganin gargajiyar na kayan ganyen shine At-Taqwah Herbal Product.
“Yana aiki don zazzabi, ciwon jiki da hawan jini. Ana gudanar da aikin ne a ofishin NAFDAC. Na fara aikin ne sama da shekara biyu a yanzu, inda suka cajeni N500,000.”
Sai dai hukumar ta musanta ikirarin Ajao.
A wani labarin kuma, Hukumar Kwastam Ta Tabbatar Da Nadin DCGs Biyar da ACGs 15
Hukumar Kwastam ta Najeriya ta tabbatar da nadin mataimakan Kwanturola Janar guda biyar DCGs da ACGs 15.
Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Misis Zainab Ahmed ce ta amince da nadin a taron hukumar na 57
Shugaban hukumar ya gargade su da su yi aiki tukuru domin samun ingantacciyar hidima.