Dan majalisar da ke wakiltar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume ya ce ya fi shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio gogewa kan harkokin majalisa.
Ndume ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels.
Da yake magana kan salon shugabancin Akpabio a majalisar dattawa ta 10, Ndume ya ce matsalata ita ce yadda ya tafiyar da lamarin, kuma abin da ya faru a karon karshe an yi rashin fahimta ko kuma an dauke shi a cikin wani yanayi. Kar ku manta na yi yaki a nan na yi wa Akpabio yakin neman zabe ba za ku iya gina gida ku lalata shi da kanku ba.
Karanta nanYa Kamata A Dinga Auna Kwarewar Alkalan Nijeriya Duk Bayan Shekara-Atiku
Babbar matsalar ita ce na fi shi gogewa idan na yi ƙoƙari in yi masa gyara,duk da cewar nine bulaliyar majalisa sai ya nuna ba haka ba.
A lokacin da yake magana ya kamata ya tuntube ni kuma bai yi haka ba,ana cikin wannan kuma sai lokacin Sallah yayi shine na fita inyi Sallah.
Ku tuna cewa Ndume ya fice daga zauren majalisar dattijai ne bayan ganawarsa da Akpabio a ranar 19 ga watan Oktoba.
A wani labarin kuma‘Yan Sanda Sun Fara Bincike Akan Mutuwar Malamar Jami’a A Jahar Neja
Ndume ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya rattaba hannu a kan kudirin da ba a bayyana ba.
A cewarsa, akwai dokoki a Burtaniya da sauran sassan duniya don magance irin wadannan matsalolin. Dan majalisar ya ce ya yi yunkurin gabatar da wasu kudirorin doka a kan haka amm an hanashi.