Naira ta ƙara raga-raga a kasuwa, ana canjin ta N1,240
Naira a jiya ta ragu zuwa N1,240 a akan dala a kasuwa daga N1,235 kowace dala a ranar Laraba.
Sai dai kuma Naira ta kara daraja zuwa N895.23 kan kowace dala a kasuwar canji ta Najeriya (NAFEM), wanda hakan ya kara tabarbare tsakanin farashin canji a hukumance da na kasuwa zuwa N344.77 kowace dala jiya daga N199.88 kowacce dala a ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnatin Tarayya ta ƙara shan alwashin kammala hanyar Abuja zuwa Kaduna
Bayanai daga FMDQ sun nuna cewa farashin canji na NAFEM ya fadi zuwa N895.23 kan kowace dala daga N1,035.12 a ranar Laraba, wanda hakan ke nuna darajar Naira 139.77.
A wani labarin kuma:NiMet yayi hasashen samun rana mai zafi da hazo
Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen samun yanayin rana da buji daga ranar Juma’a zuwa Lahadi a fadin kasar.
Hasashen yanayi na NiMet da aka fitar ranar Alhamis a Abuja ya yi hasashen za a yi wata ƙura a ranar Juma’a a yankin arewa.