Naira ta yi raga-raga a Kasuwa, ana canjin ta Naira 456.50 akan Dala
A ranar Juma’a ne dai Naira ta yi faduwa inda ake canjin ta Naira 456.50 akan Dala a kasuwar masu zuba jari da masu fitar da kayayyaki.
Adadin ya nuna raguwar kashi 0.05 cikin 100, idan aka kwatanta da N456.25 da aka yi canjin ta a ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Yadda Ɗumbin Al’umma suka tarbi Peter Obi a Bayelsa
farashin ya rufe kan N451.38 zuwa dala a ranar Juma’a.
Canjin canjin N452 zuwa Dala shine mafi girman farashin da aka samu a cinikin yau kafin ya daidaita akan N456.50.
Ana siyar da Naira kan dala 440 kan dala a kasuwar ranar.
An sayar da jimillar Naira miliyan 155.86 a wajen masu saka hannun jari da masu fitar da kayayyaki a hukumance a ranar Juma’a.
A wani labarin kuma: Yadda Jam’iyyar PDP taci zarafin wani Ɗan Majalisar PDP a Zamfara
Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum a jihar Zamfara, Suleiman Abubakar Gummi ya yi ikirarin ci gaba da tursasawa da muzgunawa ‘yan bangar siyasa da ake zargin jiga-jigan jam’iyyar APC na jihar ne ke daukar nauyinsu.
Da yake zantawa da manema labarai a Gusau, babban birnin jihar, Gummi ya bayyana zargin cewa wani jigo a jam’iyyar APC a garin Gummi mai suna Maikwarya Gummi yana daukar nauyin ‘yan baranda domin muzguna masa da kuma tursasa shi.