Tsohon Shugaban Majalisar Dattijai ta Najeriya Bukola Saraki yayi kira ga Gwamnatin Tarayya data ajiye sabbin dabarun yaƙi na zamani, wajen magance matsalolin tsaro a kasar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Saraki ya fitar, a yayinda yake taya murna akan bikin murnar ranar Tunawa da Ƴan Mazan Jiya.
KARlabaANTA WANNAN LABARIN: Mahaifiyata ce ta sanyani in Kashe Ƙanena domin tsafin neman kuɗi — Wani ɗan Yahoo ya tabbatar
Tsohon shugaban Majalisar Dattijai yace gwamnati dole ta maida rayukan ƴan Najeriya ya zamanto su ta baiwa fifiko, wajen maida hankali akan yaƙi da matsalar tsaro.
Yace ƙasar dole ta inganta ayyukan jami’an ta, domin suna aiki tuƙuru wajen magance mutuncin Najeriya.
“A yau muna tunawa da sadaukarwa ta ƴan mazan jiya mata da maza a faɗin ƙasar, wanda suka bada rayuwar su, lokacin su, jininsu domin jindaɗi ƴan ƙasa, ” Saraki ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa Yusuph Olaniyonu ya fitar.