By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce burin takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike ya fi bukata a matakin kasa, yana mai cewa Najeriya za ta yi sa’ar samun shi a matsayin shugaban kasa.
Mohammed ya ce duk da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban kasa a 2023, Wike ya tsaya tsayin daka don ceto Najeriya daga halin kuncin da gwamnatin koli mai ci ke ciki.
Ya bayyana bukatar ‘yan Najeriya su yi tunanin baiwa Wike damar yi musu hidima a matakin kasa.
Mohammed ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da aikin ginin gadar sama ta Rumukwurushi-Elimgbu a karamar hukumar Obio/Akpor ta jihar Ribas, ranar Litinin.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Wike kan harkokin yada labarai, Kelvin Ebiri, ya fitar kuma ya rabawa manema labarai.
Ya ci gaba da cewa, idan har jihar Rivers ta yi sa’ar samun Wike, ‘yan Nijeriya za su fi sa’ar samun mutum mai hangen nesa na sanin yadda ake amfani da kayan aiki wajen inganta rayuwar ‘yan kasa.
“A madadin kowa da kowa a nan, ina so in gode muku (Wike) saboda ina fatan za a ba ku damar kawo irin wannan hangen nesa zuwa matakin kasa inda za ku iya zuwa ku ba da gudummawar kason ku. ” in ji Mohammed.
Sannan ya kara da cewa “Lokacin da wasu gwamnonin wa’adi na biyu suka shagaltu da shirin komawa gida, wannan mutumin ma yana fasa sabbin iyakokin kasa, yana yin sabbin ayyuka, yana ba da lokaci da kuma kudaden da za a iya bayarwa a lokacin mulkinsa,” in ji shi.
A nasa jawabin, Wike ya ce gwamnatinsa na bin ta ne a matsayin wani nauyi da ya rataya a wuyan mutanen Rivers wajen gudanar da ayyukan jin dadin jama’a da ayyuka masu inganci da za su inganta rayuwarsu.
Ya bayyana cewa Rumukwurushi-Elimgbu Flyover shine gadar sama ta 10 kuma wani bangare ne na alkawurran da gwamnatin sa ta yi wa jama’a.
Kazalika Wike ya tabbatar da cewa za a kammala nan da watanni 10 masu zuwa domin an riga an biya kashi 80 cikin 100 na kudin kwangilolin ga dan kwangilar, Julius Berger Nigeria PLC.