Nan ba da jimawa ba za a shawo kan rikicin PDP – Hassan Hyet
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kaduna, Felix Hassan Hyet, ya bayar da tabbacin cewa da zarar jam’iyyar ta kafa kwamitin yakin neman zaben 2023, za a shawo kan rikicin da ke cikin jam’iyyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ruguza tsarin ilmi ne biyan ASUU Albashi – Jigon APC, Lukman
DAILY POST ta rahoto cewa an samu rashin jituwa kan sakamakon zaben fidda gwani na jam’iyyar da kuma nadin dan takarar gwamna Ifeanyi Okowa.
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar da yake jawabi a wajen wani taron kasa da GLAD Initiative tare da hadin gwiwar jam’iyyar PDP, suka shirya a Abuja ranar Asabar, ya bayyana cewa rashin jituwa kan zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar na iya faruwa amma ya jaddada cewa nan ba da dadewa ba za a warware domin ci gaban dukkan mambobin jam’iyyar zuwa babban zaben 2023.
A cewarsa, jin bacin rai ya kan kasance a duk lokacin da jam’iyya ta yi zaben fidda gwani, mutum zai yi tsammanin wasu da ke tunanin za su yi nasara amma ba za su yi murna ba.