NANS ta yabawa Kyari kan gyaran matatar man Fatakwal
Kungiyar dalibai ta kasa NANS, ta yabawa babban jami’in gudanarwa na kamfanin man fetur na kasa, NNPC, Malam Mele Kyari, bisa fara aiki a matatar mai ta Fatakwal, inda ta ce muhimmin mataki ne na farfado da man fetur a kasar da masana’antar iskar gas.
Kungiyar daliban, a cikin wata sanarwa da shugaban majalisar dattawa ta NANS, Kwamared Akinteye Afeez, ya fitar, ta bayyana cewa gyara da fara aiki a matatar zai rage dogaro da albarkatun man fetur da ake shigowa da su daga kasashen waje.
KARANTA WANNAN LABARIN: An naɗa Jega shugaban kwamitin gudanarwar jami’ar Nasarawa
“Wannan matakin ya nuna wani muhimmin mataki na farfado da bangaren mai da iskar gas na kasarmu da kuma bunkasa tattalin arzikinmu.
Gyara da fara aiki a matatar man ba wai kawai zai samar da guraben ayyukan yi ba, har ma zai taimaka wajen rage dogaro da kayayyakin man fetur da ake shigo da su daga kasashen waje.
A wani labarin kuma:Kayi Abinda Ya Dace Na Zaftare Kashi 50 Na Kuɗaɗen Sufuri – Peter Obi Ga Tinubu
Ɗan takarar shugaban kasa a 2023, Peter Obi, a ranar Juma’a ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu kan rage kashi 50 cikin 100 na farashin sufuri.
Obi ya ce matakin farko da gwamnatin Tinubu ta yi na taimaka wa talakawa mataki ne mai kyau.