Da Alama Karamar magana na shirin zama babba.
Jaruman fim ɗin nan mai dogon zango mai suna Daɗin Kowa wanda tashar talabijin ɗin Arewa 24 take haskawa a duk mako, wato Stephanie da Nasir na shirin angwancewa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Yan Fashi Sun Sace Takalman Da Kuɗinsu Ya Kai Dalar Amurka Dubu Goma Sha Uku 13,000 Amma kuma Wari Ɗaya Wato Duk Dama Suka Sace.
Tashar Arewa 24 ce dai ta wallafa hotunan nasu samfurin ‘pre wedding pictures’ aka kuma rubuta ‘Kar ku bari a baku labari’ a kasan hotunan.
Bayan waɗan nan hotunan tashar talabijin ɗin ta saka wani bidiyo wanda shima dai yake ɗauke da hotunan Nasir da Stephanie masu nuna alamar soyayya da kaunar juna da kuma nuna alamar angwancewa.
Tun farko dai Nasir da Stephanie sun kasance ma’aurata a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ wanda Tashar ta Arewa TV take haskawa a duk mako.
Hotunan da bidiyon da tashar Arewan ta saka a shafin ta Facebook ya karaɗe lungu da saƙo na kafafen sada zumunta na zamani musamman na Facebook, TikTok da sauran su.
Da yawa daga waɗan da suka bibiyi hotunan da Kuma bidiyon a shafukan sada zumunta daban daban sun bayyana ra’ayoyinsu akai.
Wasu na cewa lallai ƙaramar magana na shirin zama Babba, yayin da wasu kuma ke musu fatan alheri.
Sai dai har i zuwa yanzu babu tabbacin ko da gaske Nasir ɗin zai auri Stephanie ko kuma shaƙuwace kawai irin ta abokanan aiki da suka taba kasancewa a matsayin mata da miji amma a wasan kwaikwayo.
A WANI LABARIN KUMA: Shahararren ɗan wasan kwaikwayon Kannywood ɗin nan da aka fi sani da Adam A. Zango ya ce yana tunanin auren kirista a matsayin matarsa.
Adam zango ya wallafa hakan ne a shafinsa na sada zumuntar zamani na Instagram yana me buƙatar neman shawarar auran kiristan ga masu bibiyar shafin nasa.
Zango wanda yake ta fama da matsalolin aure, wanda da yawa mutane suke cewa yana da auri-saki sakamakon yawan aure da yake yi sannan kuma babu jimawa sai ya saki wacce ya aura.