Gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma ya bayyana kudirin gwamnatinsa na ci gaba da inganta hukumar kula da ma’aikata ta jihar Imo da kuma sadaukar da kai ga jin dadin ma’aikatan gwamnati.
A nasa tsokaci kan gudanar da shugabanci nagari, Gwamnan ya bayyana nasarori da dama da gwamnatinsa ta samu a ma’aikatan gwamnati, wadanda suka hada da gyaran sakatariyar jiha jigilar jama’a kyauta zuwa da komowa daga wajen aiki magani kyauta da sauransu.
A cewar Gwamnan Ina so ka sani cewa ina daraja gudunmawar da sadaukarwar da ka bayar. Gwagwarmayar ku da jajircewarku na da muhimmanci wajen ciyar da ci gaban gwamnati da jiharmu.
KARANTA NANZamu Karawa Alkalai Albashi Domin Su Daina Karbar Cin Hanci–Tinubu
Ina tabbatar muku da cewa babu wani ma’aikacin gwamnati da za a ci zarafinsa saboda amfani da hakkinsa na zabe. Mu ci gaba da hada kai don gina jihar Imo mai karfi da wadata.
Ya kuma ba su tabbacin jajircewarsa wajen magance matsalolin tsaro a jihar da ke da nasaba da siyasa. Don haka ya tabbatar da tsaro da jin dadin dukkan mazauna jihar.
Ma’aikatan da suka cika da farin ciki kan aiwatar da karin girma da aka yi musu da dai sauransu, sun gabatar da jawabai ga Gwamnan domin nuna godiya ga dimbin nasarorin da aka samu a Sakatariyar da Jiha.
Shugaban ma’aikata, Barr. Raymond Ucheoma ya yabawa Gwamnan kan dimbin ayyukan da ya yi wa ma’aikatan da har yanzu ba a kwatanta su da sauran gwamnatocin baya.
A WANI LABARIN KUMAKa Gyara Asibitoci A Maimakon Rushe Mana Gidaje–Mazauna Abuja Ga Wike
Bugu da kari, wasu manyan sakatarorin dindindin sun nuna jin dadinsu ga Gwamnan bisa wannan karamci da ya yi na samar da yanayi mai kyau ga ma’aikatan Imo don ci gaba da yi wa gwamnati da jama’a hidima.