Tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, APC, na kasa kuma tsohon gwamnan jahar Nasarawa Abdullahi Adamu ya sanar da yin murabus daga harkokin siyasa.
Adamu ya ce yana fama da rashin lafiyar harkokin siyasa, don haka yaga akwai bukatar yin ritaya.
Karanta nanDattijon Ƙasa, Ina Maka Fatan Tsawon Rai – Tinubu Ga Buhari A Bikin Cikar Sa Shekaru 81
Ya yi jawabi ne a ranar Asabar a wajen kaddamar da wani littafi mai suna ‘Progressive Governance, Showcasing The Achievements of Mai Girma Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa 2019 – 2023’, wanda Abdullahi Tanimu ya rubuta.
Abdullahi ya kuma bukaci al’ummar jihar Nasarawa da su marawa Gwamna Abdullahi Sule baya,domin ya cika burinsa na kawowa jahar gagarumin cigaba ta kowane bangare.
Adamu ya ce Sule ya karfafa nasarorin da magabata suka samu tare da inganta su a matsayinsa na gwamna.
A wani labarin kumaTsaro:Masu Bayar Da Tallafin Magunguna Na Barazanar Ficewa Daga Jahar Zamfara
A cewar Adamu ni ba mai ritaya ba ne kawai amma na fita daga duk wasu harkoki na siyasa,domin yanzu ba lokacina bane don haka naga cewar ya kamata in baiwa wasu waje domin suma su bayar da tasu gudunmawar inji shi.
Don haka ku gafarta mini, ba zan yi wata magana ta siyasa da ta wuce neman karin goyon baya ga gwamnan jihar ba.
Yana bukatar dukkan addu’o’in ku da fatan alheri don samun nasarar ciyar da jahar gaba kamar yanda ya fara a yanzu.