Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC, a ranar Asabar, ta kwace kayayyakin da wa’adin su ya kare da kuma wadanda ba su da rijista da suka kai sama da Naira miliyan 15 a Neja, Daily Nigerian ta rawaito.
Daraktan shiyyar Arewa ta tsakiya na NAFDAC, Shaba Mohammed, ne ya bayyana hakan a yayin wani samame da aka kai wasu harabar wuraren kasuwancin sayar da magani guda 24 a karamar hukumar Bida ta jihar Neja.
KARANTA WANNAN: Najeriya Ta Doke Senegal, Ya Yin da Ta Lashe Kofin Kwallon Kwando Na Mata
“Mun fara ziyarar aikinmu na yau da kullum zuwa karamar hukumar Bida, inda muka kai samame harabar wuraren kasuwanci guda 24 da suka hada da kantunan magunguna da manyan kantuna.
“A yayin farmakin, an kama wasu kayayyakin da wa’adin su ya kare da kuma wadanda ba su da rijista, ciki har da magunguna.
“Wasu daga cikin manyan kantunan na dauke da kayan shaye-shaye marasa rijista da wadanda wa’adin su ya kare, kayan shaye-shaye, man kayan lambu, taliyar spaghetti, man tumatur da kayan kwalliya wadanda suma aka kama.
“Kimar kudin kayayyakin da aka kama sun haura Naira miliyan 15,” in ji shi.
Mista Mohammed ya bayyana cewa a yayin atisayen, an rufe manyan kantuna biyu da kantunan magunguna guda biyu saboda rashin daidaito a kasuwancinsu.
Ya ce hukumar ta NAFDAC ta gayyaci wadanda abin ya shafa zuwa Minna domin yi musu tambayoyi, inda ya ce za a tura wasu daga cikin su zuwa ofishin jami’an tsaro domin ci gaba da bincike, dangane da laifin da suka aikata.
Daraktan ya shawarci jama’a da su rika bincikar duk wani samfurin da suka saya da kuma lokacin karewar wa’adin sa, ko yana da aminci na lafiya wajen sha.
“Tabbatar cewa kwanakin da ke cikin samfuran kayayyakin ba a yi musu alama ba.
“Muna kuma so mu yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga jama’a da su rika kai rahoton duk wani mutum da ake zargi da aikata munanan ayyuka ga ofishin NAFDAC mafi kusa don daukar matakin da ya dace,” inji shi.
Ya godewa Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, bisa taimakon hukumar wajen gudanar da ayyukanta a yankin.
NAN
A wani labarin kuma, Nijar: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Tinubu da ECOWAS Su Binciko Zabin Siyasa da Diflomasiyya
Majalisar Dattawa a ranar Asabar ta shawarci Shugaba Bola Tinubu, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka, da ya binciko hanyoyin diflomasiyya da na siyasa don tunkarar juyin mulkin jamhuriyar Nijar.
Majalisar dattijai a cikin wani kudiri da shugaban majalisar, GodsWill Akpabio ya karanta, bayan zaman sirri na sa’o’i biyu, ya kuma bayyana cewa shugaban kasar bai nemi majalisar dattawan ta amince da cewa kasar ta shiga yaki ba.