Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da yunkurin jigilar buhuna 16 na tabar wiwi zuwa kauyen Ndayako da ke karamar hukumar Mokwa a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar DSP Wasiu Abiodun,shi ne wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Minna.
Abiodun ya ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar 6 ga watan Satumba, 2023, bisa ga sahihan bayanan da jami’an ‘yan sandan da ke aiki a sashin Mokwa suka samu.
KARANTA WANNAN: FG ta Gayyaci NLC Wata Ganawa don Tattauna Muhimman Batutuwa Kan Yajin Aiki
Wadanda ake zargin sun hada da; Auta Umar Saidu mai shekaru 25, Mohammed Bala dan kimanin shekaru 52, dukansu ma zauna Mokwa.
A cewarsa, “An kama Auta a kauyen Muwo a lokacin da yake kokarin jigilar buhuna 16 na tabar wiwi zuwa kauyen Ndayako.
“A yayin da ake yi masa tambayoyi, Auta ya amsa cewa Bala ne ya aiko shi ya karbi buhunan daga hannun wani Lawali, wanda ya kawo kayan daga jihar Ondo.”
Ya bayyana cewa daga baya an kama Bala kuma dukkansu sun amsa cewa ana sayar da buhunan, kuma sun shafe kusan watanni takwas suna wannan sana’ar tare.
An mika wadanda ake zargin zuwa SCID Minna kuma an gurfanar da su a gaban kotu domin su girbe abinda suka shuka.
A wani labarin kuma, Shari’ar Gwamnan Zamfara: Kotu ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci
Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Zamfara da ke zamanta a Sokoto ta sanya ranar Litinin 18 ga Satumba, 2023 domin yanke hukunci.
Kotun a cewar rahoton za ta yanke hukuncin ne kan karar da tsohon gwamnan jihar a yanzu haka ministan tsaro Alhaji Muhammadu Bello Matawallen Maradun ya shigar yana kalubalantar sahihancin zaben da ya kawo mai girma Dauda Lawal a matsayin gwamnan jihar.