Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Elrufai ya ce dan takarar shugaban kasa na jamiyyar Labour Party Mr Peter Obi ba zai iya taba lashe zaben 2023 ba, balle burinsa na son zama shugaban kasa ya tabbata.
Malam Elrufai ya ce Peter Obi bashi da yawan magoya bayan da ake bukata dan takara ya samu balle a dinga la’akari da shi cikin sahun yan takara, hakan ya sanya yake kallon sa kamar wani jarumi a masanaantar fina finaI ta Nollywood.
KU KARANTA: Masu Hankali Sun San Cewa Idan Ka Ilimantar Da Yariya Ka Ilimantar Da Al’umma — Osinbajo
A don haka ne ya ce yanzu rigegeniyar ta zama tsakanin APC ne da PDP, yayin da sauran jamiyyaun zasu zama yan kallo a ranar zabe.
Yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na TVC ya ce kuru’un karamar hukuma daya a Kaduna zasu iya rinajye an kuri’un Anambra baki daya, yayin da yake da magoya baya kaso biyar cikin 100 a Kano, 2 cikin dari a Katsina, da kuma kaso daya cikin dari a jihar Sokoto.
A wani labarin kuma: Shugaba Buhari Yayi Baƙin Ciki Matuƙa Da Wahalar Da Ƴan Najeriya Ke Sha Kan Sababbin Kuɗi – Minista
Ministan kuɗi, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa shugaba baya jindaɗin wahalar da ƴan Najeriya ke fuskanta saboda sababbin kuɗaɗen naira.
Zainab Ahmed ta bayyana hakan ne yayin da take magana a wajen wani taron ministoci a faɗar shugaban ƙasa. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.