Gabanin wasan da Najeriya zata buga da Ghana a ranar Talata, 29 ga watan Maris a filin wasa na MKO Abiola dake Abuja, Sanata Orji Uzor Kalu, ya sayi tikiti 5,000 ga masu sha’awar kwallon kafa da za su goyi bayan Super Eagles.
Kalu, wanda ke wakiltar mazabar Abia ta Arewa a majalisar dattawa, ya bayyana haka ne a safiyar Lahadi ta shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewa hakan ya fito ne ta hanyar gidauniyar sa ta Orji Uzor Kalu.
Ya ce za a raba tikitin ne a kofar filin wasan da karfe 3 na rana.
A cewarsa, “A matsayina na Wani ginshiki a fannin wasanni, Ina fatan Eagles su sanya murmushi a fuskokinmu ta hanyar lashe wasan.”
Super Eagles za ta fafata da Black Stars ta Ghana a wasa na biyu na Neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022 bayan Ghana ta karbi bakuncin wasan farko a filin wasa na Baba Yara da ke Kumasi a ranar Juma’a inda aka tashi babu ci.
Wanda ya yi nasara a karawar ta biyu zai sa zama daya daga cikin kasashe biyar na Afirka da zasu je gasar cin kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci a watan Nuwamba.
Comments 1