Wani abokina masoyi kuma mai daraja wanda ya taba zama jakadanmu a wata kasa ta Turai, wanda ke da ‘yan uwa da alaka mai karfi a jamhuriyar Nijar.
Kuma kwararre kan harkokin tsaro da leken asiri, ya shaida min cewa jarirai kusan 40 ne ke mutuwa kowace rana. a Nijar sakamakon katse musu wutar lantarki da muka yi inji Femi Falana babban lauya a Najeriya.
A cewarsa, wadannan jariran suna mutuwa ne a asibitoci da babu injina a fadin kasar sakamakon rashin wutar lantarki da kuma man fetur da za su iya amfani da janaretonsu.
Wani Dr. Abdoul Djibou, kwararren likita dan kasar Nijar ne ya tabbatar da hakan a wata hira da yayi da yan jarida.
Jaridar Vanguard sun rubuta cewar wata a Jamhuriyar Nijar, Dr. Abdoul Djibou,ya bayyana samun rahotanni daga asibitin yankin Dosso da asibitin Cominak game da karuwar mace-macen jarirai a baya-bayan nan.
KARANTA NANMun Kashe Fiye Da Biliyan 7 Wajen Gyaran Tashar Motar Gombe-Gwamna Inuwa
A cewarsa, sama da jarirai 40 ne ke mutuwa a kullum a Nijar tun bayan da gwamnatin Najeriya ta katse wutar lantarki ga Nijar tare da rufe iyakokinta.
Ya shafi asibitoci masu karamin karfi saboda sun kasa yin amfani da incubators da sauran kayan aikin tallafi don taimaka wa waɗannan jariran.
Har ila yau, ya bayyana cewa rufe iyakokin ya sa asibitoci kusan ba za su iya samun albarkatun man fetur ba musamman dizal da man fetur don samar da wutar lantarki da injinan su.
Wannan baya ga wahalhalun da jama’a ke fama da su a Nijar ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta sake duba matakin da ta dauka duk da cewa kungiyar ECOWAS ta mara mata baya.
Ya kuma jaddada nasa ra’ayin, ya yi imanin cewa tattaunawar da ake yi da shugabannin mulkin sojan za ta haifar da sakamako mai kyau, ya kuma jaddada bukatar a kara matsa kaimi a maimakon buga gangunan yaki da kuma tabbatar da tsauraran takunkuman da aka kakaba mata a halin yanzu da ya durkusar da tattalin arzikin kasar musamman bangaren lafiya.
A WANI LABARIN KUMADole ‘Ya’yanka Suyi Karatu A Jami’o’in Najeriya-ASUU Ga Ministan Ilimi
Katsewar ya samo asali ne sakamakon tsauraran takunkumin tattalin arziki da tafiye-tafiye da kasashen yankin suka kakabawa kasar bayan da wasu sojoji suka hambarar da shugaban kasar a watan da ya gabata.
Takunkumin na yin illa ga jama’a tare da tashin farashin kayayyaki, mazauna yankin ba sa iya samun kudi cikin sauki, da kuma mutanen da ke zaune a cikin duhu.shi.