Daga: Abbas Yakubu Yaura
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen samun yanayin hadari da ruwan sama daga ranar Litinin zuwa Laraba.
Sakamakon yanayi na NiMet da aka fitar ranar Lahadi a Abuja ya yi hasashen cewa za a yi ruwan sama kamar da bakin kwarya da sanyin safiya a sassan Jihohin Sokoto, Zamfara, Kebbi da Katsina a ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/an-kama-wasu-malamai-2-da-suka-rubuta-takardar-koke-akan-dg-na-narict/
A cewarta, ana sa ran za’ayi ruwa da rana a wasu sassan Bauchi, Kaduna da Taraba.
“Ana sa ran da sanyin safiya idan Allah ya amince a yankin Arewa ta tsakiya za’ayi ruwan. Wanda kuma daga bisani ne ake sa ran samun ruwan sama a wasu sassan babban birnin tarayya, Nasarawa, Neja da jihar Filato.
” Ana tsammanin za a yi yanayin hazo a kan manyan biranen Kudu da na bakin teku.
“A cikin sa’o’in rana da yamma, ana sa ran za a yi ruwan sama a wasu wuraren sassan Jihohin kudancin Najeriya Imo, Ebonyi, Abia, Edo, Enugu, Ribas da Cross River yayin da ake sa ran za a yi ruwan sama a sassan Legas, Oyo, Ogun da Bayelsa,” in ji ta.
NiMet ta yi hasashen cewa sararin samaniyar ranar Talata zai kasance cikin yanayin hasken rana jefi jefi a yankin arewacin kasar da yuwuwar samun tsawa a sassan jihar Taraba da safe.
Ta yi hasashen samun tsawa a wasu sassan jihohin Kebbi, Zamfara, Sokoto, Kaduna, Kano, Borno, Gombe, Adamawa da Taraba da yammacin ranar.
Hukumar ta yi hasashen cewa yankin Arewa ta tsakiya zai kasance cikin gajimare da samun tazarar hasken rana da safe.
Kazalika NiMet ta yi hasashen zazzafar tsawa a wasu sassan Filato da babban birnin tarayya da kuma jihar Neja da rana da kuma yamma.
Sannan tace hasashen yanayin ya nuna za’a samu gajimare a duk yankin kudanci Najeriya da safe.
Hukumar ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama a sassan jihohin Enugu, Imo, Ondo, Edo, Ogun, Legas, Ribas, Cross River da Akwa Ibom da rana da yamma a ranar Talata.
“A ranar Laraba, gajimare tare da takaitattun hasken rana sun yi hasashe kan yankin Arewa tare da yiwuwar samun tsawa a Jihohin Gombe da Taraba da safe.
” Ana sa ran yiwuwar samun tsawa a sassan jihohin Jigawa da Bauchi da Zamfara da Kaduna da Kano da Katsina da rana da kuma yamma.
“Ana sa ran samun tsawa a sassan jihar Neja . Ana sa ran za a yi tsawa a sassan Filato da Nasarawa da kuma Binuwai da rana da kuma yammacin ranar Laraba,” inji ta.
Hukumar ta yi hasashen biranen cikin kasa da kuma garuruwan da ke gabar tekun Kudancin kasar zasu kasance cikin gajimare da safe.
An yi hasashen idan Allah ya amince za a yi ruwan sama a sassan Oyo da Ogun da ma dukkan jihohin da ke gabar teku da rana da kuma yamma.
A cewarta, don rage yawan yashewar ruwa da ambaliya fiye da yadda aka saba, ya kamata a yashe magudanun ruwa da hanyoyin ruwa daga dukkan wasu tarkace da zasu kawo cikas domin tabbatar da kwararar ruwa cikin walwala.
“An shawarci ma’aikatan jiragen sama da su sami sabbin rahotannin yanayi daga NiMet don ingantaccen shirin su a cikin ayyukansu,” in ji shi.
NAN