Kungiyar kwadago ta Kasa NLC a ranar Talata ta bayyana cewa ta dakatar da yajin aikin da ta shirya yi a duk fadin kasar nan ranar Laraba domin nuna rashin amincew da cire tallafin man fetur. Kamar yadda jaridar PUNCH ta rawaito
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa NLC ta bayyana dalilin na ta na janye yajin aiki da cewa saboda gwamnati ta nuna a shirye ta ke ta tattauana da ku?! samar da “hanyoyi masu kyau don dakile tasirin munufofin tallafin”
KARANTA WANNAN An Yanka Ta Tashi: NLC Za Ta Tsiduma Yajin Aikin Gama Gari
Ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a karshen taronta na gaggawa na kasa a ranar Talata.
“Bisa la’akari da yanayin tsatin zamantakewar al’umma, zabukan da suka gabata da kuma bukafar tabbatar da zaman lafiya a Kasa, sakamakon haka, taron NEC ya warware lamurin”
“Don yabawa da kwazon shugabancin kungiyar wajen gudanar sa aiki da NEC ya bata, da nunawa gwamnatin tarayya bukatar bin dokar Kasa”
“Musamman yadda ta shafi biyayya ga Hukunce-hukuncen kotuna da rashin biyayya ga dokar kasafin kudin 2023“.
A Wani Labarin Kuma Gwamnan Sokoto Ya Bada Tallafi Ga Wadanda ‘Yan Bindiga Suka Farmaka
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya bayar da tallafin kudi da hatsi ga iyalan wadanda ‘yan bindiga suka kashe a ranar Asabar din da ta gabata.
Ya kuma bayar da gudunmawar kudi ga wadanda suka jikkata da kuma wadanda suka yi asarar dukiyoyinsu yayin hare-haren.