- Ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya kulla hadin gwiwa da hukumar NAFDAC domin dakile amfani da miyagun kwayoyi a fadin kasar nan.
- NSA ta ce amfani da miyagun kwayoyi na haifar da rashin tsaro a kasar nan.
- NAFDAC ta yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su tona asirin masu sayar da miyagun kwayoyi a kasar nan.
A ranar Laraba ne ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya kulla hadin gwiwa da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa domin dakile amfani da miyagun kwayoyi a fadin kasar nan,Punch ta rawaito./
A cewar sanarwar da Daraktan dabarun sadarwa, Ozoya Imohimi, Ko-odinetan Cibiyar Yaki da Ta’addanci ta kasa, ONSA, Admiral Yaminu Musa (mai ritaya), ya ce amfani da miyagun kwayoyi na haifar da rashin tsaro a kasar nan.
KARANTA WANNAN: An Kubutar Da ‘Yan Mata Masu Ciki 6 Daga Hannun Wasu Da Ake Zargi da Safarar Su
Sanarwar ta kara da cewa, “Shaye-shaye na daya daga cikin abincin da ke kara haddasa rashin tsaro a Najeriya, don haka bukatar karfafa hadin gwiwa tsakanin ma’aikatun gwamnati da hukumomin da abin ya shafa, musamman NAFDAC, domin tinkarar wannan matsala, dole ne a dawwama don samun kwanciyar hankali da juriyar al’umma.”
Babbar Daraktan NAFDAC, farfesa Mojisola Adeyeye, ta yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su tona asirin masu sayar da miyagun kwayoyi, inda ta kara da cewa an lalata makomar matasa da dama ta hanyar amfani da kwayoyi.
Ta yi alkawarin cewa ci gaba da hadin gwiwar hukumarta da NCTC a cikin ONSA zai haifar da sakamako mai kyau don amfanin Najeriya.
A wani labarin kuma, Kotu Ta Ɗaure Wani Mai Siyayya A Kasuwannin Kauye Da Jabun Kuɗi A Kano
An gurfanar da wani matashi a gaban kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a unguwar Kwana huɗu Kano, bisa zarginsa da mallakar kuɗin jabu.
Wanda ake zargin mai suna Abdurra’uf Muhammad mai shekaru 45, mazaunin Garin Iyayi dake ƙaramar hukumar Ningi a jihar Bauchi.