Hukumar Jami’an tsaro ta Sibil difens ta Kasa reshen Jahar Kwara ta cafke wasu mutane biyu ɓarayin shanu a Oro-Ago ta Ƙaramar Hukumar Ifeolodun ta Jahar.
Waɗanda aka kama suna ɗaya daga cikin wanda suka kasance suna addabar Al’ummomin Jahar Kwara a kwanakin da suka gabata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya Ta Samar Da Yanayi Ga Masana Kimiyya
A cewar Mai magana da yawun Hukumar Jami’an tsaron Farin Kaya ta Sibil difens Babawale Afolabi biyu daga cikin mutane uku masu satar shanun an kama su ne a ranar Talata wanda ƴan sintiri na ƙungiyar Miyetti Allah suka yi, a lokacin da suka kai hari a rigar Raura Mohammed a gidan sa dake Oro-Ago a lokacin da ɗaya daga cikin ƴan tawagar ya tsere zuwa daji.
Ya bada sunan waɗanda aka kama da suna Abdullahi Ide da Kadiri Babuga, inda na ukun ake kiran sa da suna Baba Sanda amma ya tsere zuwa daji.
Babawale yace ” masu satar shanun sun farmaki makiyayin da muggan makamai, kuma suka barshi cikin mummunan hali, kafin su tafi da shanu guda uku da kudin su yakai Naira miliyan 1.5