Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC, reshen jihar Kano, ta ce ta cafke akalla mutane 93 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar tsakanin watan Janairu zuwa Maris.
Mista Adamu Salihu, Kwamandan NSCDC na jihar ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Kano ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: IGP Ya Baiwa Iyalan ‘Yan Sandan da Suka Mutu Sama da Miliyan N84m
Salihu ya ce an kama wadanda ake zargin ne da laifin sata, barna da cin amana da sauransu.
“Daga cikin wadanda ake tuhuma 93, 29 an gurfanar da su a gaban kotu, 57 da ake tuhuma suna kan bincike kuma mun samu hukunci guda bakwai a cikin wannan lokaci,” inji shi.
Kwamandan ya nanata kudurin NSCDC na karewa da kuma kiyaye duk wasu muhimman kadarori da ababen more rayuwa na kasa.
Ya bukaci mazauna yankin da su tallafa wa jami’an tsaro da bayanan tsaro masu amfani don kiyaye zaman lafiyar jihar, ya kara da cewa tsaro ya zama alhakin kowane dan kasa.
A wani labarin kuma, NSCDC Ta Yi Holin Wasu Dillalan Tabar Wiwi Uku
Jami’an Rundunar tsaron farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen jihar Ekiti, ta gurfanar da wasu mutane uku da suka kware wajen tacewa da siyar da wasu abubuwan da ake zargin tabar wiwi ne a garin Ado Ekiti.
Wadanda ake zargin, Agbekeye Ayomide mai shekaru 22, Oladimeji Akintomiwa dan kimanin shekaru 21, da Agbeleye Beulah 20, an kama su ne a Zone 1 Olorunda Adebayo da ke Ado babban birnin jihar inda suke siyar da kayayyakin.