NUT, NULGE: Wike ya ƙulla yarjejeniya da malaman makarantun Abuja da ke yajin aiki
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya bayyana yarjejeniyar da ya kulla da kungiyar malamai ta Najeriya, NUT, reshen Abuja, kan yajin aikin da malaman firamare ke yi a babban birnin kasar.
Ministan babban birnin tarayya Abuja ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata a Abuja lokacin da ya gudanar da wani taro da sarakunan babban birnin tarayya Abuja da kuma shugabannin kananan hukumomi.
KARANTA WANNAN LABARIN:Tinubu ba shi da shirin canjawa fadar shugaban ƙasa matsuguni – Fadar Shugaban Kasa
Shugaban Majalisar Gargajiya na FCT da kuma Onah na Abaji, Dokta Adamu Baba Yunusa, ya jawo hankalin Wike ga halin da ake ciki a babban birnin tarayya Abuja.
Yunusa ya kuma ja hankalin Ministan kan batun yajin aikin ma’aikatan kananan hukumomin FCT na NULGE, inda ya amsa cewa an warware matsalar.
Ministan ya ce ya gana da kungiyar NUT da kuma kananan hukumomin, inda suka amince da cewa FCTA za ta biya kashi 40 na basussukan da kananan hukumomin ke bin su duk wata, yayin da sauran kananan hukumomin kuma za su biya sauran 60 bisa dari.
“Haka kuma da NULGE. FCTA ta dauki sama da kashi 40, a bar su su biya kashi 60. A cikin watanni uku, hudu, da mun gama biya; duk sun yi farin ciki.”
A wani labarin kuma:Gwamna Abdulrazaq ya ziyarci ‘yan uwan Nabeeha da aka sako a Abuja
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara, a ranar Laraba ya ziyarci iyalan Nabeeha Alkadiriyah da ke Abuja wadanda masu garkuwa da su suka sako ‘ya’yansu da suka yi garkuwa da su bayan an biya su kudin fansa.
A yayin ziyarar, gwamnan ya dan dauki lokaci tare da tattaunawa da ‘yan matan da aka kwato ‘yancinsu daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.