Obi bai ce uffan ba kan Kalaman Mbaka na cewa Marowa ci ne — Cewar Hadimin sa
Mai Taimakawa Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Labour Party Peter Obi, akan Kafafen Yaɗa Labaru Valentine Obienyem yace maigidan sa bai yi martani kan kalaman da Rabaran Fr Ejike Mbaka yayi akan sa ba.
Jaridar The PUNCH ta ruwaito cewar Mbaka yayi magana inda ya bayyana Obi a matsayin ‘Marowaci’ wanda ya janyo hankalin mutane musamman masu amfani da Kafafen Sadarwa na Zamani akan kalaman.
A Wani rahoto da Kafafen Yaɗa Labaru (ba Dimokuraɗiyya ba) sun ce tsohon Gwamnan Jahar Anambra ya yi jawabi akan kalaman Mbaka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jadawalin Gasar Premier League Na Shekarar 2022/2023
A cikin wata sanarwa da Majiyar mu ta samu a ranar Alhamis, Obienyem yace Obi bai ce ƙala akan maganganun da Faston yayi, kuma bazai yi jawabi akan haka ba, ko wata sanarwa.
Sanarwar tace “hankalin mu yakai ga wani jawabi da aka alaƙanta shi da Mr Peter Obi cewa ya yiwa Fr. Ejike Mbaka Martani.
“Muna so mu sanar domin kowa ya sani cewa Mr Peter Obi bai yi martani ba, kuma baya da niyyar yin martani akan kalaman.
“Muna shawartar kowace kafa dake da yunƙurin wallafa wannan bayanai, dasu tuntuɓi gaskiya lamarin daga ofishin Mr. Peter Obi akan Kafafen Sadarwa.
Comments 1