A halin yanzu an rufe wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati a Abuja domin nuna goyon bayansu ga yajin aikin kwanaki biyu da kungiyar kwadago ta Kasa NLC ta ayyana a fadin kasar, inji rahoton jaridar The PUNCH.
Wakilinmu da ya ziyarci sakatariyar gwamnatin tarayya a safiyar ranar Talatar nan tare da wasu manyan wurare kamar gidan rediyo mai farin jini da ke da wasu hukumomi a karkashin ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a ta kasa.
Ya lura cewa wuraren ba kowa a yayin da ma’aikata suka yanke shawarar komawa gida.
KARANTA WANNAN Gwamnatin Tarayya Ta Mayarwa Da Falana Martani Kan Yajin Aikin NLC
Bankunan da ke yankunan da aka zagaya su ma an kulle su.
Wakilinmu da ya ziyarci daya daga cikin manyan bankunan kasuwanci da ke sakatariyar gwamnatin tarayya, ya shaida cewa ba za a gudanar da harkokin banki ba saboda yajin aikin da NLC ta shiga.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta ruwaito cewa, a ranar Juma’ar da ta gabata ne kungiyar NLC a cikin wata sanarwar da ta fitar wacce ta samu sanya hannun shugabanta na kasa Joe Ajaero tare da sakatarenta, Emmanuel Ugboaja, ta ce an yanke shawarar daukar matakin ne biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya da Tinubu ke jagoranta.
Bisa kin yadda a tattauna da masu ruwa da tsaki na ƙungiyar da aka tsara a kan ƙoƙarin da ake yi na rage tasirin cire tallafi man fetur
Tuni ma kungiyoyin kwadagon da suka shirya a watan Agusta suka gudanar da zanga-zangar ta yini guda wadda ta hana gudanar da ayyuka a manyan biranen kasar nan.
A yayin da take lissafo wasu daga cikin dalilan da ya sa za ta tara mambobinta domin rufe kasar baki daya, cibiyar ta zargi ‘yan sandan da yin kawanya a shedikwatar kungiyar ma’aikatan ta kasa.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Bisa zargin cin zarafin ma’aikata a jihar Imo. Tsoma bakin gwamnatin jihar Abia a harkokin kungiyar kwadago, da neman rugujewar sabon ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike da dai sauransu.
A Wani Labarin Kuma Ko Kaɗan Tinubu bai damu da hukuncin kotu ba – Kakakin Fadar Shugaban Ƙasa
Mai magana da yawun shugaban kasa Bola Tinubu, Ajuri Ngelale ya yi ikirarin cewa shugaban nasa bai damu da hukuncin kotun zaben shugaban kasa ba.
Ngelale ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.