Gwamnan Delta kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Sanata Ifeanyi Okowa, ya yi kira ga gwamnatin tarayya, kungiyoyi da kuma daidaikun jama’a da su kai dauki ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Okowa ya dakatar da harkokin siyasa na wani dan lokaci domin komawa jihar sa, domin tantance irin tasirin ambaliyar ruwan ga wadanda lamarin ya shafa tare da yin gangamin tallafawa wadanda abin ya shafa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sokoto: Hadimin Tambuwal Da Mataimakin Shugaban Jamiyyar PDP Sun Sauya Sheka
Kazalika Okowa Ya ziyarci wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke fadin jihar.
Ya jajanta wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar, ya kuma ba da tabbacin gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa musu har sai sun samu damar komawa gidajensu bayan lamarin..
“Ambaliya ce mai girman gaske da ta tarwatsa mutane da yawa kuma dole ne in gode wa dukkan mutane daban-daban da suka zo nan.,” in ji shi.
A WANI LABARIN KUMA: Asibitin Reshid Shekoni Na Shirin Zama Asibitin Koyarwa Na FUD
Gwamnatin tarayya ta karbi asibitin koyarwa na Reshid Shekoni dake birnin Dutse a jihar Jigawa.
Ministan Lafiya, Dakta Osagie Ehanire da Gwamnan Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar ne suka sanya hannu akan takardar yarjejeniyar.