Osimhen ya lashe kyautar gwarzon Dan wasan Afirka na Duniya
Victor Osimhen ya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya na Afirka a gasar kwallon kafa ta Ghana.
Dan wasan Napoli na Italiya ya samu kuri’u mafi yawa a gaban dan wasan Liverpool Mohamed Salah da na Manchester City Riyad Mahrez da kuma Yassine Bounou na Morocco.
KARANTA WANNAN LABARIN:Matsalar Taro: Sarkin Minna Ya Dakatar Da Hawan Durbar Na Babbar Sallah
Osimhen ya lashe kyautar ne a karon farko kuma shi ne dan Najeriya na farko da ya samu wannan matsayi.
Dan wasan mai shekaru 24 a baya ya lashe kyautuka guda biyu a kakar wasa ta bana.
Dan wasan na Najeriya ya lashe kyautar dan wasan da ya fi zura kwallaye a gasar Seria A sannan kuma an ba shi kyautar dan wasan da ya fi kowa taka leda a gasar.
Osimhen kuma shi ne aka fi so ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Afrika.
A wani labarin kuma:Mashahurin Farfesan Jarida A Najeriya Ya Rasu
Shahararren Farfesan jarida a Tsangayar koyon karatukan jarida da Nazarin Watsa Labarai (FCMS) na Jami’ar Jihar Legas, Lai Oso, ya rasu yana da shekaru 67 a duniya.
Rahotanni sun ce, lamarin ya faru ne a wani mummunan hadarin mota da ya rutsa da shi a hanyarsa ta komawa Legas, daga Jami’ar Jihar Delta, Abraka; a ranar Asabar, 24 ga watan Yuni, 2023.