Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta sake dage ziyarar yakin neman zaben ta a jihar Kebbi.
Jam’iyyar ta ce dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai ziyarci jihar ce a ranar 28 ga watan Janairu, kamar yadda NAN ta ruwaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan baranda Sun Farmaki Ayarin Atiku, An Kwantar Da Mutane Da Dama A Asibiti
Sani Dododo, shugaban kwamitin yada labarai na Jam’iyar a jihar kan yakin Neman zabe ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi ranar Laraba.
Dododo ya ce an dauki matakin ne bisa sauye sauyen wasu tsare-tsare da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ya yi.
“Yakin neman zaben shugaban kasa, wanda aka shirya gudanarwa a ranar Asabar, 12 ga Nuwamba, za a gudanar da shi ne yanzu a ranar Asabar, 28 ga Janairun shekarar 2023.
“Duk kwamitocin da aka kafa za su ci gaba da ayyukan shirye shiryen gudanar da yakin neman zabe sannu a hankali.
“Ina so in yi amfani da wannan kafar domin bayyana nadama kan dage wannan ziyara na dan takarar PDP; duk da haka, ina so in roki dukkan magoya bayansa da su ci gaba da shirye-shiryen taron.
“Hakazalika, kwamitin ya yi gargadi da kakkausar murya cewa ‘yan jam’iyar su daina yada jita-jita da kuma maganganun da ke iya haifar da rashin hadin kai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar,” in ji shi.
A WANI LABARI KUMA: Da Dumi:Dumi: Kotu Ta Kori Dan Takaran Gwamnan Labour Party Na Enugu
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kori Chijioke Edeoga a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour a jihar Enugu.
Idan za a iya tunawa cewa Evarest Nnaji, wanda aka fi sani da Odengene ya garzaya kotun Abuja domin kalubalantar zaben fidda gwani da aka gudanar a watan Mayu wanda ya samar da Chijioke a matsayin dan takarar jam’iyyar.