Peter Obi ya yi tsokaci kan zanga-zangar nuna rashin amincewa da sakamakon zabe da mata suka yi tsirara
Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben da aka kammala kwanan nan, Peter Obi, ya mayar da martani kan zanga-zangar da mata suka yi a jihar Nasarawa kan sakamakon zaben.
Mata a karamar hukumar Akwanga da ke jihar Nasarawa sun tube tsirara a jiya domin nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben gwamna da aka gudanar a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN:Kashi 77 na matan Najeriya na amfani da man bleaching – Bincike
Matan sun yi ikirarin cewa an sace musu wa’adin da aka ba su, kuma sun dage cewa dole ne a kirga kuri’unsu.
Obi, a wani martani da ya fitar a shafinsa na Twitter a daren Juma’a, ya ce manufar zabe ta sha kaye ne yayin da aka hana jama’a zabinsu.
“Na ci karo da wani faifan bidiyo mai ban tausayi, mai ratsa zuciya inda matan Nasarawa suka gudanar da zanga-zangar rashin jin dadinsu da sakamakon zaben,” inji shi.
Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour ya ce babban rashin adalci ne yayin da ‘yan kasar suka kasa samun damar kada kuri’a a cikin ‘yanci, gaskiya da adalci.
Ya koka da yadda matan da ya kamata a kare hakkinsu a yanzu an tauye su.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana Abdullahi Sule na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Nasarawa da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Jami’in tattara kuri’u a jihar Farfesa Ishaya Tanko, ya ce dan takarar jam’iyyar APC ya samu kuri’u 347,209 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa kuma dan takarar jam’iyyar PDP, David Ombugadu, wanda ya samu kuri’u 283,016.
A wani labarin kuma:Kashi 77 na matan Najeriya na amfani da man bleaching – Bincike
Jigon jam’iyyar a APC, Femi Fani-Kayode, ya alakanta ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, da Labour Party, Peter Obi, da kirkiran rahotannin da ke cewa, zaben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya gana da babban alkalin kotun Nigeria, CJN, Olukayode Ariwoola, a Landan.
Daily post ta ruwaito cewa, Fani-Kayode ya ce abin da Atiku da Obi da mabiyan su ke yi abin kyama ne.