Daga: Ibrahim Hassan Hausawa
Sallah babba a bana sai san Barka ga wasu, yayin da wasu kuma daga cikin al’umma ke ci gaba da dangana sakamakon yanayin rayuwa da suka tsinci kansu a ciki.
A jihar Kano, wani abu da ba a saba gani ba, shine yadda wajen masu siyar da kaji ya bunkasa, wato dai hada hada ta karu, sakamakon yawaitar al’umma masu son siyan kajin.
Dimokuraɗiyya ta zanta da wasu daga cikin wadanda suka je domin siyan kajin, a kasuwar kaji ta kasuwar Kurmi, ga kuma abinda suka shaida mana kamar haka:
“Sunana Auwal Abdullahi, nazo siyan kaji ne saboda gudun kada yara na a gobe suga ko’ina anan harkar nama amma banda gidan su, don gaskiya bana ba zan iya siyan abun layya ba.
To Koh me yasa?
Haba Malam Kamar ba a garin nan kake ba, yanzu ace rago kadai ana maganar Naira dubu 70, 80, 100, har da Ɗari da doriya, wanda kuma kai kadai ma cinye shi zakai, kaga dole mu siyi kaji don dai gudun zama haka ba tare da an ci naman ba”.
Dimokuraɗiyya ta sake tuntubar guda cikin masu siyar da kajin kan yanayin kasuwa ga abinda yake cewa:
“Magamar gaskiya Malam Sallah irin ta bana Allah ya ci gaba da maimaita mana, saboda wallahi mu dai ba abun da zamu ce sai godiya ga Allah,”
Shin a iya yau kayi cinikin ya kai nawa?
Chab! Ai ba zan iya kididdige maka nawa nayi ba, amma dai na san sun doshi dubu ɗari 3, zuwa 250 haka, maganar gaskiya ba, saboda duk daya mukan siyar da ita dubu 4 da dari 500, zuwa abinda yayi sama.”
Wannan dai sabon abu ne a iya cewa a jihar Kano, a jajiberen Sallah Babba a dinga siyan kaji maimakon tumakai, ko shanu.
Da yawa dai cikin Kanawan na kokawa ne kan yadda kudade suka yi musu karanci a hannu, yayin da ma’aikata ke kukan rashin albashi daga Gwamnati.