Wata dalibar Jami’ar Jihar Yobe da ke Damaturu, Maryam Lawan Goroma, a ranar Alhamis, ta fadi ta rasu jim kadan bayan ta kammala rubuta jarabawar ta,Punch ta rawaito.
Kafin rasuwarta, an ce tana cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Ranar Litinin A Matsayin Hutu
Wani abokin karatunta mai suna Bukar Maisandari ne ya bayyana hakan a shafin sa na Facebook.
Ya kara da cewa marigayiyar ta fadi kasa kwatsam kuma an tabbatar da mutuwarta jim kadan bayan faduwarta
Ya ce: “Inna Lillahi Wa’inna Ilaihi Raji’uun. Naji a zuciyata na samu labarin rasuwar yar ajinmu Maryam Lawan Goroma.
“Tana cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali har zuwa yau da yamma, kwatsam ta fadi kuma aka tabbatar da mutuwarta jim kadan.
“Allah Ta’ala Ya gafarta mata kurakuranta. Allah yasa Al-Jannah Firdausi ta zama matabbata ta karshe a gareta.
“Mafi tausayina ga danginta da abokanta da dukkan abokan karatunta na Injiniya.
“Allah ya baku ikon jure hakurin wannan rashin. Ameen.”
A wani labarin kuma, Sarkin Kano Ya Nada Sabbin Hakimai Guda Shida
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL, ya nada sababbin Hakimai guda shida.
Da yake jawabi lokacin nadin Hakiman, Mai Martaba Sakin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace an nadasu Sarautun ne bisa cancantarsu da irin gudunmawar da suke bayarwa a cikin al’umma.
Wadanda aka nada Sarautun sun hadar da Alhaji Abbas Maje Ado Bayero a Matsayin Bauran Kano da Alhaji Kabiru Ado Bayero a Matsayin San Turakin Kano da Alhaji Umar Ado Bayero wanda aka nada shi Yariman Kano.
Sauran sune Alhaji Tijjani Ado Bayero a Matsayin Zannan Kano da Alhaji Auwalu Ado Bayero a Matsayin Sadaukin Kano da Alhaji Ado Ado Bayero a Matsayin Cigarin Kano.