Ralf Rangnick ya dage cewa babu bukatar cire Harry Maguire daga mukamin kyaftin din Manchester United duk da cewa ya yarda cewa ya ga “wasu Halayen na rauni daga Dan wasan”.
An duba Maguire a kan wasanni da yawa a kasa a wannan kakar kuma wani bangare na magoya bayan United sun ba da shawarar a amshe Kambun Kyaftin daga hannunsa.
“Ina tsammanin lokacin da ya dawo bayan raunin da ya samu ya yi rawar gani sosai, ya buga wasa mai kyau da West Ham,” in ji Rangnick.
“A cikin wasanni biyun da suka gabata, eh ya sami rauni kwarai da gaske, a karawar da Southampton da kuma lokacin da muka zura kwallo a ragar Burnley, amma shi ne kyaftin din mu kuma ban ga dalilin canza hakan ba.”
Tsohon kociyan kungiyar Ole Gunnar Solskjaer ya nada Maguire kyaftin din United a watan Janairun shekarar 2020, watanni biyar bayan ya koma Old Trafford a kan kudi fam miliyan 80 daga kungiyar Leicester.
Tuni dai ya buga wasanni 132 a kungiyar kuma Rangnick ya ce zai dauki lokaci kafin dan wasan na Ingila ya saba da sabuwar hanyar taka leda a United.
Ya kara da cewa, “Dan wasa ne da ya kamata ya ci gaba, ya samu sauki, kamar sauran ‘yan wasa.
“Hanyar da muke buga wasa a yanzu sabuwa ce a gareshi saboda a cikin tawagar kasar Ingila ya saba buga baya, a nan Manchester United kuma, amma har yanzu ba ya taka rawar gani.
“Wannan kuma wani sabon abu ne a gare shi kuma zai ɗauki ɗan lokaci kafin ya saba da hakan, don daidaitawa da hakan.”